1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

China da Philippines na nuna wa juna dan yatsa

October 22, 2023

Kasashen China da Philippines na zargin junansu bayan da wasu jiragen ruwa biyu suka ci karo a Tekun kudancin China.

Jiragen ruwan kasashen China da Philippines
Jiragen ruwan kasashen China da PhilippinesHoto: Armed Forces of the Philippines/AP/picture alliance

Wani jirgin ruwa da ke tsaron gabar ruwan China ya yi taho mu gama da wani jirgin dakon kaya da dakarun sojin Philippines suka bayar da kwangilar kai abinci da sauran kayan bukatu ga dakarun da ke tashar Thomas Shoal, inda gwamnatin Beijing ke ikrarin nan ma yankin ruwanta ne.

Gwamnatin Philippines dai ta zargi masu tsaron tekun Chinar da alhakin aukuwar lamarin inda ta ce jiragen ruwan China ba su mutunta yarjejeniyar MDD na dokar kan teku ba.

To sai dai masu gadin tekun China sun zargi dayan bangaren da kutsa kai cikin ruwan China wanda hakan ya sabawa dokar kasa da kasa kan kaucewa cin karo a teku.

Karin bayani: Tada jijiyoyin wuya tsakanin China da Philippines

Kasashen biyu na na ci gaba da nuna juna dan yatsa kan yankin ruwan. Kasar Amirka da ta dade ta na dasawa da Philippines ta yi tir da matakin China.