1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaChaina

China: Nazarin sayar da TikTok ga Elon Musk

Abdullahi Tanko Bala
January 14, 2025

Jami'an China na duba yiwuwar sayar da kamfanin TikTok na Amurka ga hamshakin atajiri Elon Musk

Hoto: Avishek Das/SOPA Images/Sipa USA/picture alliance

Kafar yada labaran Bloomberg ya ruwaito cewa hukumomin China na duba yiwuwar sayar da kadarorin TikTok a Amurka ga Elon Musk. Kafar sada zumuntar na fuskantar wa'adi ko dai a sayar da ita ga wani a cikin Amurka ko kuma a rufe ta baki daya a kasar. Tattaunawar sayar da TikTok din na matakin farko ne a yanzu.

Kafar sadar zumuntar mallakar kamfanin ByteDance na da hedikwata ne a China

A baya bayan nan an yi ta tada jijjiyar wuya a Amurka kan kamfanin na China bisa fargabar saba dokar kundin adana bayanai.

Gwamnatin Amurka ta yi zargin cewa China na amfani da TikTok wajen tatsar bayanai da yin leken asiri kan masu amfani da dandalin tare ma da yada farfaganda. Zargin kuma da gwamnatin China da kamfanin ByteDance suka musanta.