China za gina haanyoyin mota da asibitoci a Ruwanda
July 23, 2018Talla
Shugaban kasar China Xi Jinping ya saka hannu a kan kwangiloli kasuwanci guda 15 da gwamnatin Ruwanda inda ya kai ziyara a mataki na biyu na rangadin da yake yi a cikin wasu kasashen Afira. Kafin ranar Larba ya isa Afirka ta ta Kudu inda zai halarci taron kasashe na kungiyar BRICS. A yarjejeniyar da shugabannin biyu na China da Ruwanda suka cimma China ta amince ta gina sabbin hanyoyin mota da asibitoci da kuma filin saukar jiragen sama a Ruwanda.