China: Alamun sassauci kan Musulmi
January 9, 2019Talla
Wannan mataki ne da ke zama alamu na cewa mahukuntan na Beijing za su iya fara sassautowa kan matakin da suke dauka kan Musulmi a yankin Xinjiang da ke yammacin China.
Rike al'ummar Uighur da Kazakh da wasu kananan kabilu a wasu sansanoni don sauya masu dabi'u lamari ne da ya haifar da nuna yatsa tsakanin Kazakhstan da China wacce ke zama babbar kawa ta fuskar kasuwanci.
Kazakhstan dai da fari taki bari 'yan jarida su yi ta yayata batun, sai dai sannu a hankali abun ya dau hankali na kasashen duniya abun da ya sanya China ke shan suka na gallazawa ga Musulmi da ke zama marasa rinjaye a kasar. Ministan harkokin wajen Kazakhstan dai ya tabbatar da batun sakin na mutane 2,000 'yan asalin Kazakh wadanda za su fice daga kasar ta China.