China ta gargadi Kanada kan Hong Kong
August 19, 2019Talla
Gabanin wannan kare kai daga gwamnatin China, an jiyo ministar harkokin kasashen wajen kasar Kanada Chyrstia Freeland da shugabar manufofin harkokin wajen kungiyar EU Federica Mogherini suna jaddada muhimmancin 'yancin fadin albarkarcin baki da kuma zanga-zangar lumana a matsayin wajibi bayan sun bayyana takaici game da yadda rikici ke kara kamari a Hong Kong.
Masu zanga-zangar dai sun ci alwashin cigaba da kyamar gwamnatin yankin har ta amince da bukatunsu, duk kuwa da irin kiraye-kirayen sulhun da kasashe ke yi wa bangarorin biyu.