Masu zanga-zanga sun yi nasara kan gwamnati
September 5, 2019![China, Hongkong: Carrie Lam](https://static.dw.com/image/50272418_800.webp)
Shugabar gwamnatin Hong Kong Carrie Lam, ta ce gwamnatin China ta yaba da hukuncin da ta dauka na janye dokar don samar da zaman lafiya a kasar da ta fada cikin rudani tun bayan sanarwar gwamnati a game da shirin aiwatar da wata ayar dokar, da za ta bata damar iza keyar masu aikata laifi zuwa kasar ta China.
Ms Lam, ta fadi hakan ne a yayin da take wata ganawa a wannan Alhamis da manema labarai. A yammancin jiya Laraba ne Shugabar ta sanar da wanann mataki a cikin wani sako Bidiyo da ta wallafa bayan da ta ce rikicin ya jefa al'ummar kasar cikin damuwa.
Carrie Lam ta kuma yi kira ga masu zanga-zanga dasu yi watsi da hanyar tarzoma da kuma hawa tebirin sulhu da gwamnati. Daga bangaren gwamnati za su dauki matakan da suka dace a cikin sauri domin maido da doka da oda a cikin yankin.