1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

China ta gudanar da gagarumin atisaye a yankin Taiwan

December 29, 2025

An shafe shekaru ana zaman doya da manja tsakanin China da Taiwan, yankin da Amurka ke goya wa baya.

Sojojin sama da na kasa da na ruwa ne suka gudanar da atisayen na ranar Litinin.
Sojojin sama da na kasa da na ruwa ne suka gudanar da atisayen na ranar Litinin.Hoto: Cheng Yu-chen/AFP/Getty Images

China ta gudanar da atisayen soji a kewayen Taiwan inda ta ce ta na killace muhimman yankuna ne na tsibirin, a matsayin gargadi ga abin da ta kira "kungiyoyin masu neman ballewa”.

Rundunar sojin kasa da ta ruwa da ta sama da kuma rundunar makamai masu linzami duk sun shiga atisayen, kamar yadda sojojin China suka bayyana.

Taiwan na bukatar zaman lafiya da China

An sanya wa atisayen suna "Justice Mission 2025”, kuma ana gudanar da shi ne kwanaki kadan bayan Amurka ta sanar da sayar wa Taiwan daya daga cikin manyan kunshin makamai mafi girma, wanda darajarsa ta kai dala biliyan 11.

Wannan mataki ya jawo zazzafar suka daga Beijing, wacce ta mayar da martani ta hanyar sanya takunkumi kan wasu kamfanonin kera makaman Amurka.

China ta kakaba wa kamfanonin Amurka 10 takunkumai

Yunkurin Taiwan na kara karfafa tsaronta a wannan shekara ya fusata Beijing, wacce ke ikirarin cewa tsibirin yankinta ne duk da cewa Taiwan na mulkin kanta.

 Ofishin shugaban Taiwan ya soki atisayen sojin na China, inda ya ce hakan tamkar kalubalantar ka’idojin kasa da kasa ne.