China ta sake atisayen soji a tekun Taiwan
August 8, 2022Talla
China ta kaddamar da sabbin atisayen soji a teku da sararin samaniyar yankin Taiwan a yau Litinin, kwana guda bayan da aka tsara kammala atisayen da suka yi mafi girma na nuna adawa da ziyarar kakain majalisar dokokin Amirka Nensi Pelosy a tsibirin a makon jiya.
Wannan mataki da China ke cigaba da dauka, na tabbatar da fargabar yuwar Beijing za ta ci gaba da matsa lamba kan tsaron Taiwan.
Ma'aikatar harkokin wajen Taiwan ta yi Allah-wadai da matakin soji da China ke dauka a kewenenta, tun dai ba yau ba ne China ke cigaba da ikirarin mallake tsibirin Taiwan, wacce ke danganta kanta yanki mai cin gashin kanta.