China ta kara tallafinta a yaki da Ebola
October 31, 2014Kasar ta bayyana cewa za ta kara yawan adadin tallafin da ta ke bayar wa a yaki da cutar Ebola, inda yanzu za ta bada Yuan miliyan 750 wato kimanin dala miliyan 123. Wannan sanarwa ta fito ne daga ma'aikatar harkokin wajen kasar ta China a yau Juma'a.
A cewar Lin Songtian, daraktan da ke kula da harkokin Afrika a ma'aikatar harkokin wajen Beijing, ya bayyana cewa akwai kuma karin ma'aikatan lafiya 200 wato karin cikin 500 da tuni aka tura wadannan kasashe da ke fama da cutar ta Ebola.
Kasar China dai na gina cibiyar kula da marasa lafiyar ta Ebola a kasar Laberiya, ginin da ake saran kammalawa cikin wata guda, ta kuma tura motoci na daukar marasa lafiya 60 da babura 100 da dubban kayan da ma'aikatan jinya ke bukata da sauran magungunan a asibitoci.