1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

China ta laftawa Amurka harajin fito na kaso 15 cikin 100

Binta Aliyu Zurmi
February 4, 2025

China a wani mataki na ramuwar gayya ta laftawa Amurka harajin kaso 15 cikin 100 na kayayakin kwal da na makamashin gas da ake higar da shi kasar daga Amurka.

USA und China (Visualisierung)
Hoto: IMAGO/Depositphotos

Karin harajin a cewar ma'aikatar kudin Beijing zai fara aiki ne a makon gobe.

Bugu da kari China ta sanar matakin fara bincike a kan kamfanin fasaha na Google. 

Wannan na zuwa ne bayan da Amurka ta laftawa China harajin kaso 10 cikin 100 na kayayakin China da ke shiga kasar ta Trump.

Kasashen China da Canada da Mexico ne suka fara samun wannan karin harajin, to sai dai Canada da Mexico tuni Donald Trump din ya dakatar da nasu karin da kwanaki 30, a cewar fadar mulkin Amurkan Trump ya bukaci kasashen biyu da su dauki matakin hana kwarar bakin haure shiga kasarsa ta barauniyar hanya da ma shigar da miyagun kwayoyi.

Karin Bayani: China da Kanada da Mexico sun mayar wa Amurka da martanin haraji