1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

China ta samu gwaggwabar riba a kayan da take fitarwa ketare

March 7, 2021

Kasar China ta sanar da samun gagarumin cinikin kayayyakin da kasashen duniya ke saya daga gare ta, shekara guda bayan bullar coronavirus wace ta kusan durkusar da dukkanin harkokin kasuwanci a duniya.

China Peking Außenminister Wang Yi
Hoto: Wang Yuguo/XinHua/picture alliance

 Bunkasar fitar da kayayyakin na China da kaso 60 cikin 100 a cikin shekara daya, ta saba da hasashen da masana suka yi na cewa China din za ta samu rubanyar cinikin kayan da take fitarwa da kaso 39 ne kawai. 


Wannan gagarumin ci gaban tattalin arziki da Chinan ta sanar a wannan Lahadi, na zama wani babban ci gaba domin a shekaru kusan sama da 20, China din ba ta samu bunkasar cinikin kayan da take fitarwa ba kamar wanda ta samu daga watan Janairun bara zuwa Fabrairun bana ba.


Galibin kayayyakin da China ta fitar zuwa kasashen ketaren sun shafi kayan lataroni da duniya ta rinka yin oda domin yin aiki daga gida sai kuma tufafi da sauran nau'i kamar takunkumin rufe hanci da shima China ta yi cinikinsa kuma ta samu gwaggwabar riba.