China ta yi alkawarin tallafwa Asusun Turai
February 2, 2012Shugaban kasar China Wen Jia bao ya ce kasarsa zata taka rawar gani wajen daidaita rikicin bashin kasashen Turai. Ya kuma ce kasarsa zata bada nata tallafin ga asusun tallafin Turai wato EFSF da ESM. Shugaban ya bayyana haka ne lokacin ganawarsa da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, wacce ta ke ziyarar ran gadi na kwanaki uku, a Bejing. Kana kuma ya ce shuwagabanin zasu gano matakan da zasu dace, kasancewar warware rikicin na Turai, abu ne mai mahimmancin gaske. A yayinda China ke alkawarin goyon bayan Kasashen Turai wajen daidaita matsalolin rukunin kasashen da ke amfani da takardar kudin na euro, Ita ma Turai ta ce zata iya kokarinta wajen rage yawan basussukanta, ta kuma gudanar da suaye-sauye a yanayin tattalin arzikinta saboda alfanun da yin hakan zai kawo, kamar yadda shugabar gwamnatin na Jamus ta Bayyana:
Takardar kudin euro a matsayin takardar kudin Turai na bai daya, ya kara karfafa kasashen Turai, ta yarda kasa kamar Jamus ta sami kyakyawar riba, kuma har ta zama kasa mai fitar da kayayyakinta zuwa sauran kasashen Turai, kuma babu shakka a tsakanin kungiyar Tarayyar Turai, abubuwa zasu kara kyautatuwa da takardar kudin na Euro
Mawallafiya: Pinado Abdu-Waba
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe