China: Yakin cinikayya bai amfani Amirka ba
June 2, 2019Talla
Wata sanarwa daga ofishin kakakin gwamnatin ta ce China ta cika akawuranta a dukkan tattaunawa goma sha daya da suka yi da Amirka kuma a shirye ta ke ta martaba su idan an cimma yarjejeniya kan cinikayyar.
Ta kuma zargi Amirka da kwan gaba kwan baya har sau uku yayin da ake tattaunawar inda ta rika bullo da wasu sabbin kudin fito da wasu dokoki da suka wuce abin da aka cimma yarjejeniya akansu.
Mataimakin ministan kasuwanci Wang Shouwen ya mayar da martani ga zargin Amirka cewa Beijin ta sauya yarjejeniya yayin da ake zagayen karshe na cimma matsaya a farkon wannan watan.
"Yace shawarwari tattaunawa ce kawai amma ba yarjejeniya. Babu wani ja baya da muka yi. Idan ana tattaunawa babu yarjejeniya sai an amince akan komai tukunna."