1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

China za ta baiwa Chen Guangcheng takardun izini yin balaguro

May 4, 2012

Sakatariyar harkokin wajen Amirka Hylari Clinton na da fatan cewar za a sami mafita a rikicin

epa03199885 Undated handout image provided by ChinaAid of blind Chinese legal activist Chen Guangcheng (R) with his family. Chen Guangcheng is under US protection in Beijing following a dramatic escape from house arrest, according to rights group ChinaAid, 28 April 2012. EPA/www.ChinaAid.org BEST QUALITY AVAILABLE +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hoto: picture-alliance/dpa

Hukumomi a ƙasar China sun ce a shirye suke su samar da hanyar ficcewa zuwa ƙasar waje ga lauyan nan, makaho Chen Guangcheng; da ke fafutukar kare hakin bil adama wanda ya sami mafuka a ofishin jakadancin Amirka a birnin Bejin.Shugabannin na ƙasar China sun ce ,Chen ya na iya ajiye buƙatar neman scolarship zuwa karatun a ƙasashen waje abinda zai bashi damar arcewa daga ƙasar.Tun farko dai lauyan ya ce na da farga akan makomar sa, da ta iyalen sa kafin ya buƙaci Amirka da ta saka baki a cikin lamarin domin zuwa hijira a can.A taron manema labaran da ta yi sakatariyar harkokin wajen Amirkan Hilary Clinton da ke yin ziyara a birnin Bejin.

Ta ce maganar kare hakin bil adama ita ce ke da mahimmanci a dangantakar da ke tsakanin su da China sannan kuma ta ƙara da cewa ta na sa ran za a sami bakin zaren rikicin akan wannan lamari na mista Chen.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar