1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

China za ta sassauta dokar hana fita

Binta Aliyu Zurmi
March 24, 2020

Sakamakon nasarar da China ta samu a fanin yaki da coronavirus, yanzu ta shirya barin mutane su koma harkokinsu. China dai ta zama abar misali ga kasashen duniya.

China Wuhan Barrieren auf Straße entfernt
Hoto: Reuters/China Daily

Hukumomi a China sun sanar da cewa za su sassauta dokar nan ta hana fita a yankin Hubei inda cutar coronavirus ta samo asali, yankin da aka shafe kusan watannin biyu karkashin wannan doka. Batun sassauta dokar zai fara aiki ne a ranar 8 ga watan Afirilu.

Wannan sanarwar na zuwa ne bayan nasarar da aka yi na kwanaki biyar ba tare da samun mutum daya da ya kamu da cutar ba. 

A share guda kuwa ana samun wasu yankunan kasar ta China da cutar ke bulla a cikinsu, ganin yadda baki ke shigowa da su daga wasu kasashen.

A ranar 23 na watan Janairu ne, kasar ta China ta ayyana dokar ta-baci na ba sani ba sabo, a yankin Wuhan musamman, wanda hakan ya taimaka wajen dakile yaduwar cutar. 

A halin da ake ciki dai al'amura sun fara komawa yadda aka saba a kasar ta China.