China za ta sayi jirage 120 samfurin Airbus daga Jamus
February 26, 2026
Kwana guda bayan ganawa da shugaba Xi Jinping na China a ziyarar aiki da ya fara a Beijin, a wannan Alhamis shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya ziyarci birnin Hangzhou da ke zama babbar cibiyar hada-hadar fasaha ta kasar China.
Makasudin wannan ziyara shi ne karfafa kyakkyawar alakar da ke tsakanin kasashen biyu a fannin tattalin arziki ta tsawon shekaru, domin neman mafita kan manufofin shugaban Amurka Donald Trump a batun cinikayya da kasuwancin duniya.
Karin bayani - Jamus da China sun karfafa alakar dangataka
Daga cikin tawagar da ke yi wa Mr Merz rakiya zuwa China, akwai jagororin manyan kamfanonin kera motoci na Volkswagen da BMW da kuma Mercedes, kuma shugaban zai leka cibiyar harkokin makamashi ta Jamus Siemens, sannan ya zarce zuwa bangaren sha'anin kirkirarriyar basira wato AI.
A ranar Laraba Mr Merz ya sanar da cewa China ta amince da sayen jiragen sama guda 120 samfurin Airbus daga Jamus.