Wani gina da ake aiki a kan shi ya ruguje a China
November 24, 2016Wani gini da ya ruguje yayin da ake aikinsa a wata cibiyar samar da wutar lantarki a kasar China, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 40 a wannan Alhamis din a yankin Jiangxi da ke Gabashin kasar a cewar kanfanin dillancin labaran kasar ta Chine nouvelle.
Da misalin karfe 7:00 na safiya ne agogon kasar China hadarin ya aufku a birnin Fengcheng yayin da ake gina wani dogon bene, inda masu aikin ceto suka isa wurin domin bayar da agajin gaggawa.
Irin wannan hadari dai na cikin kanfanoni a kasar ta China ya zama ruwan dare gama duniya, inda a shekarar da ta gabata, wasu ababe da suka fashe a birnin Tianjin da ke yankin Arewa maso Gabashin kasar, suka yi sanadiyyar mutuwar mutane 170, kuma Shugaban kasar ta Sin Xi Jinping ya sha alwashin cewa hukumomin kasar za su dauki darasi kan iri-irin wadannan hadaruka da ke afkuwa.