1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Christine Lagarde na ci gaba da ziyara a Najeriya

December 20, 2011

Shugabar asusun bada lamuni ta duniya wato IMF ta na ganawa da yan kasuwa a birnin Lagos, bayan da ajiya ta gana da shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a Abuja, inda ta ce ta gamsu da shirin tattalin arzikin Najeriya

President Goodluck Jonathan arrives for the ruling party primary in Abuja, Nigeria, Thursday, Jan. 13, 2011. Delegates of Nigeria's ruling party began voting Thursday night to pick its presidential candidate, choosing between honoring a power-sharing agreement by selecting a Muslim or endorsing the oil-rich nation's current Christian leader. (AP Photo/Sunday Alamba)
Shugaban Najeriya Goodluck JonathanHoto: AP

A wani abun da ke zaman ziyarar tat a farko a tarrayar nigeria da safiyar Litinin shugabar hukumar lamuni ta duniya ta IMF tace ta gamsu da matakan gwamantin Nijeriya take dauka na kaiwa ga sake farfado da tattalin arzikin kasar.

A cikin kaffa kaffa da ma dar dar a bangaren talakawan tarrayar Nijeriya ne dai Christine Lagarde da ke zaman shugabar hukumar lamuni ta IMF ta iso Abuja domin fara ziyarar ta farko a nahiyar Afirka ziyarar kuma da hukumar tace na da burin kafa sabon shafin dangantaka a tsakanin IMF da sauran kasashe masu tasowa a nahiyar Afirka dama wajen ta.

Lagarde din dai ta shaidawa yan jarida cewar ta zo sauraro ne da kuma duba yiwuwar bada shawara in hali yayi, ga gwamantin da a cewar kasar tana bisa hanya ga kokarin sake dora kasar bisa tafarkin tattalin arziki mai inganci.

“Hukumar IMF kawa ce kuma mun dade muna kawance da tarrayar Nigeria na lokaci mai tsawo. Mun kuma yi gyaran fuska ga cibiyoyin mu mun zo ne mu saurara mu fahimta muka bada shawara in an nema, mun bada shawara ta kwarraru ga kokarin kyautata aiyyukan bankuna a Nijeriya kuma muna farin ciki da irin nasarar da aka samu.”

Shugabar asusun bada lamuni na IMF Christine LagardeHoto: dapd

To sai dai in har agajin na hukumar lamuni ya zamo abun alheri ga bankunan kasar ta Nijeriya , daga dukkan alamu akwai sauran tafiya a tsakanin hukumar da samun amincewar al'umar tarrayar Nijeriya da ke mata kallo irin na bakar aniya da ta taimaka ga lalata tattalion arzikin kasar a cikin shekaru na 1980.

Ana dai kallon hukumar da tilasta rage darajar kudin kasar na Naira da kuma tsuke bakin aljihun da yai sanadiyar talauta al' umar kasar ta Nijeriya da dama.

Ko bayan nan dai Lagarde din na ziyarar tata ne a dai dai lokacin da hankalin al'umar kasar ke kan muhawarar zare tallafin man fetur , muhawarar kuma da ake ta'allakawa da shawarwarin hukumar da ta dade tana taka rawa cikin harkokin kasar a bayan fili.

To sai dai kuma a cewar Dr Okonjo Iweala dake zaman ministar kudin kasar ta Nijeriya, rawar hukumar ya canja kuma kidan nata ma ya kama hanyar sauyawa.

“Hukumar ta IMF dai ta sauya daga abun da mutane suka sani a baya. IMF ta bamu dama mu tsara manufofin mu: in mun nemi agajin su wajen shawara ta kwararru su bamu, in kuma mun yi shiru to su yan goyon baya ne fa kawai.”

Babban bankin Najeriya

To sai dai koma wace irin rawa take shirin takawa a kasar dai ana kallon ziyarar a matsayin goyon baya ga sabon shirin gwamantin kasar na sake farfadowar tattalin arzikin da ke neman gwara kan al'ummar kasar baki daya. Shirin kuma da a cewar shugabar mai kyaune.

“Mun dauki tsawon lokaci muna nazarin shirin san a sake farfado da tattalin arziki na transformation agenda. Da sabbabin sauye sauyen da ke neman inga tattalin arzikin Nigeria.kuma zan fada a matsayi na na shugabar hukumar IMF na yi matukar gamsuwa da aiyyukan day a ke jagoranta da kuma irin karfi da zumar sat a sake farfado da tattalin arziki da samar da aiyyukan yi da kuma kyautata harkokin noma. Abune mai ban sha'awa.”

Ana dai saran Lagarde din zata gana da shugabannin majalisun tarrayar kasar biyu, da ‘ya'yan kungiyoyi masu zaman kansu kafin daga baya ta je birnin Ikko domin taka rawa a wani taron nazarin makomar Afirka a cikin rikicin tattalin arziki na kasa da kasa.

Ranar Talata ne dai ake sararn shugabar zata tsallaka ya zuwa jamhuriyar Niger domin c ci gaba da zirara tata ta kwanaki hudu.

Mawallafi: Ubale Musa

Edita: Umaru Aliyu