Ci-gaba a sasanta rikicin Siriya
May 4, 2016 Hukumomin kasashen biyu, sun kuma nemi tsagaita wutan ya shafi har birnin Aleppo inda bangarorin biyu ke fafatawa 'yan kwanakinnan. Rasha da Amirka dai sune ke iya fada aji a rikicin Siriya, inda Amirka da kawayenta kamar su Saudiyya da Katar ke marawa 'yan tawaye baya, yayin da kasar Rasha ke tallafawa gwamnatin Siriya.
Dama dai kasar Rasha ta bayyana cewa bisa ga dukkan alamu ana iya komawa tattauna rikicin kasar Siriya a watanda muke ciki. Ministan harkokin wajen kasar ta Rasha Sergei Lavrov, shi ne ya bayyana haka a wannan Laraba. Lavrov ya ce kawo yanzu sasantawar da ake yi ba ta kai ga tattaunawar gaba da gaba, a bisa abinda ya kira cikas da 'yan tawaye ke kawowa. Yana mai cewa tsauraren sharruda da bukatun 'yan tawayen ba abu ne da zai taimaka wa tattaunawar da ake yi.