Bala'iAsiya
Ci gaba da aikin ceto a Nepal
September 8, 2026
Talla
A kasar Nepal alkaluman wadanda ambaliyar ruwa ta halaka sun kai 1,357 yayin da wasu kimanin 5,326 suka bace aka eci gaba da nema. Hukuma kula da bala'o'i ta kasar ta fitar da alkaluman a wannan Talata, makonni biyu bayan samun iftila'in ambaliyar ruwan.
Ci gaba da aikin ceto
Sannan a kasar China mutane 43 wannan ambaliyar ruwa ta halaka yayin da wasu 519 suka bace, a cewar kafofin yada labaran kasar.
Kwararru daga kasashen China da Indiya da Koriya ta Kudu sun hade da na Nepal wajen aikin taimakon wadanda suka tagayyara makonni biyu bayan bala'in gami da ci gaba da aikin ceton masu sauran kwana.