1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaKenya

Ci gaba da tashin hankali a Kenya

June 27, 2024

'Yan sanda sun tarwatsu masu gangami a lokacin da suka yi ayari domin zuwa fadar gwamtanin kasar yayin da masu bore ke ci gaba da yin zanga-zanga a kan wani kudirin doka.

Hoto: Monicah Mwangi /REUTERS

 Duk da alkawarinda gwamnatin Kenya ta yi na janye wannan kudurin doka da majalisar dokokin kasar ta amince da shi na kare-karen kudin haraji da ya bar baya da kura, matasa na ci gaba da yin bore ga gwamnatin kasar. Dama dai matasan sun lashi takobin dorawa daga inda suka tsaya a wannan Alhamis din na jerin zanga-zangar da suka kwashe ranaku suna yi, lamarin dai ya fi kamari a babban birnin kasar Nairobi, sakamakon matasan da suka yi jerin gwano domin zuwa gidan gwamnati. A birnin Mombasa, kungiyoyin bata gari sun shige cikin masu boren inda suka yi yunkurin fasa shaguna domin kwasar ganima. An kara tsaurara matakan tsaro a birnin tare da rufe wasu hanyoyin da ke kewaye da majalisar dokokin kasar da masu boren suka kutsa a ranar Talata. Rahotanni sun yi nuni da cewa, a yanzu haka mutum bakwai ne aka kwantar a asibiti sakamakon raunin da suka ji yayin zanga-zangar a yammacin birnin Homa Bay. Sai dai matasan sun ce ba za su yi kasa a gwiwa ba har sai hakkarsu ta cimma ruwa.

Masu zanga-zanga na son shugaba Ruto da ya yi marabus

Hoto: Daniel Irungu/EPA

Har yanzu ba ta bayyana karara ba ko masu boren za su janye daga kan tititunan kasar duk da cewa shugaba Ruto ya mayar da wukarsa cikin kube, kwana guda bayan da arangama tsakanin masu zanga-zangar da jami'an tsaro ya yi sanadin mutuwar mutane 23. Matasa da dama ne suka ce sun fidda tsamannin da salon kamun ludayin mulkinsa, inda suka fara kira da ya sauka daga kan madafu ikon kasar.