1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaba da boren ƙin jinin gwamnati a Masar

January 28, 2011

Matasan na Masar na ci gaba da takun saka da sojoji da ke ɗauke da makamai, duk kuma da dokar ta ɓaci da shugaba Hosni Mubarak ya kafa.

Matasan Masar a lokacin da suke ƙalubalantar SojojiHoto: picture-alliance/dpa

Shugaba Hosni Mubarak na Masar ya kafa dokar ta baci a birane uku na ƙasar da suka haɗa da alƙahira da Alexandiriya da kuma Suez, domin daƙile zanga-zangar nuna ƙin jinin gwamantinsa da ke ciki da ƙamari. Tuni dai sojoji da kuma 'yan sanda da shugaba Mubarak ya danƙa wa nauyin aiwatar da wannan mataki, suka fara amfani da tsinin bindiga, wajen tarwatsa gungun masu zanga-zanga da ke neman ganin bayan gwamnati da ke ci yanzu.

Shi dai shugaba Mubarak da ya shafe kusan shekaru 30 a kan karagar mulki, ya na ci gaba da shan alwashin ladabtar da duk wani ɗan ƙasar da zai fito kan titi domin ƙalubalantar gwamantinsa. ƙasashen yammacin duniya ciki kuwa har da Amirka da kuma Jamus sun fara nuna damuwa game da tauye 'yancin talakawan Masar na gudanar da zanga-zanga. Sai dai masu boren sun banka wa cibiyar jam'iyar da ke kan karagar mulki wuta, sa'o'in ƙalilan kafin jawabi da shugaba Mubarak zai yi wa al'uma ta kafar telebijin..

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu