1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben Najeriya: Ci gaba da kada kuri'a

February 26, 2023

Ana ci gaba da kada kuri'a a wasu sassan Najeriya, kwana guda bayan gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya.

Zaben Najeriya 2023
Yayin da aka fara tattara sakamakon zabe a NAjeriya, a wasu sassan sai an sake zabenHoto: Benson Ibeabuchi/AFP

Rahotanni sun nunar da cewa, al'umma na ci gaba da kada kuru'a a garin Yenagoa da ke jihar Bayelsa da kuma wasu sassan jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin kasar. Kawo yanzu dai babu alkaluma a hukumance da suka bayyana adadin 'yan Najeriya da ba su samu damar kada kuri'a a jiya Asabar ba. An dai samu matsaloli a wasu sassan kasar a jiya Asabar da suka hada da tangardar na'ura da kuma zuwan jami'an zabe da ma kayayn aiki a makare. Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Kasar INEC ta ce ana sa ran kamalla tattara sakamakon zaben a wannan Lahadin. Sakamakon farko-farko na zaben na nuni da cewa 'yan takara uku ne ke kan gaba wadanda suka hada da Bola Ahmed Tinubu na jam'iyya APC mai mulki da Atiku Abubakar na babbar jam'iyyar adawa ta PDP sai kuma Peter Obi na jam'iyya Labour. Nan da kwanaki biyar ne hukumar ta INEC za ta bayyana wanda zai maye gurbin Shugaba Muhammadu Buhari da ke kawo karshen wa'adin mulkinsa na biyu bayan shafe shekaru taakwas a kan karagar mulki. Ana dai ganin akwai jan aiki a gaban wanda zai gaji Shugaba Buhari wajen sauya kasar da ke fama da matsaloli da suka shafi tsaro da ma tatattalin arziki.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani