1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaba da luguden wuta a Gaza ka iya zama laifukan yaki

Binta Aliyu Zurmi
November 2, 2023

Hukumomin kare hakkin bil Adama na Majalisar Dinkin Duniya sun ce ci gaba da luguden wuta da Isra'ila ke yi a kan wuraren da suke da cinkoson fararen hula a Zirin Gaza ka iya zama manyan laifukan yaki.

Gazastreifen I UNRWA
Hoto: Mahmud Hams/AFP/Getty Images

Hakan na zuwa ne bayan wani sabon hari da dakarun Isra'ila suka kai karo na biyu a babban sansanin 'yan gudun hijira da ke Jabalia.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antoniyo Guterres ya bayyana matukar damuwa kan ruwan bama-bamai da dakarun Isra'ila ke ci gaba da yi a Gaza duk da kiraye-kirayen neman a tsagaita wuta.

Karin bayani: Isra'ila ta yi watsi da tsagaita wuta a Gaza

 

Sai dai Isra'ila ta ce sojojin nata sun kai harin ne ga mayakan Hamas, wani shaidun gani da ido ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na Faransa AFP munin wannan harin a sansanin da mutane ke neman mafaka.

Ma'aikatar lafiya ta Hamas ta bayyana cewa tun bayan da Isra'ila ta kaddamar da martanin ramuwar gayya, ya zuwa yanzu Falasdinawa sama da mutum 8,700 ne suka mutu, mafi akasarinsu mata da kananan yara.