1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci-gaba da murƙushe 'yan zanga-zanga a Siriya

August 18, 2011

Majalisar Ɗinkin Duniya za ta tura wani rukuni zuwa Siriya domin duba halin rayuwa a wuraren da gwamnati ke ɗaukar matakan soja akan 'yan zanga-zanga

Masu zanga-zanga a birnin LatakiyaHoto: picture-alliance/dpa

Gwamnatin Siriya na ci gaba da ɗaukar matakan soji domin murƙushe masu boren nuna adawa da ita -dalilin da ya sa a Laraba (17.08-2011) Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce za ta tura wani rukuni zuwa ƙasar ta Siriya nan ba da daɗewa ba da zai kimanta halin da mutane ke ciki a wuraren da gwamnati ke ɗaukar matakan na soji. Har yanzu gwamnatin ta Siriya ta ƙi ta ba wa Majalisar Ɗinkin Duniya damar tura wani rukuni zuwa ƙasar duk kuwa da kiraye kirayen da babban sakataren majalisar, Ban Ki-moon ya shafe watannin yana yi mata da ta ba da damar yin hakan. 'Yan fafutukar kare haƙƙin bil Adama sun ce aƙalla mutane 36 suka rasa rayukansu a birnin Latakiya cikin kwanaki huɗu da suka gabata.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Aliyu