Gano gawarwakin bakin haure a gabar ruwan Libiya
August 27, 2015Talla
Rahotanni sun nunar da cewa jirgin ruwan sintiri na kasar Sweden da ke aiki a hukumar tsaron gabar teku da kasashen Tarayyar Turai suka kafa wato Triton ne ya gano gawarwakin yayin da yake bakin aiki a gabar ruwan Libiya. Sai dai da aka fara ceto wasu bakin hauren 439 a cikin kwale-kwalen kafin daga bisani aka gano gawarwakin a cikinsa. Kungiyar kula da 'yan gudun hijira ta kasa da kasa ta bayyana cewa sama da mutane 2,000 ne suka hallaka a teku cikin wannan shekarar ta 2015 a kokarin da suke na tsallakowa Turai.