1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kanada da Amirka na neman tsara huldar kasuwanci

Salissou Boukari
August 31, 2018

Har ya zuwa yammacin ranar Alhamis kasashen Amirka da Kanada ba su kai ga cimma matsaya kan batun sabunta yarjejeniyar kasuwancin ta bai daya ta (Alena) ba.

USA Washington Chrystia Freeland
Hoto: Getty Images/AFP/N. Kamm

A baya dai tuni Amirka ta kai ga cimma matsaya ta yarjejeniyar tare da kasar Mexico tun a ranar Litinin da ta gabata.  Sai dai masu tattaunawa na kasashen biyu za su sake komawa kan teburin tattaunawar a safiyar wannan Jumma'ar da ke a matsayin rana ta karshe domin cimma wannan matsaya kamar yadda shugaban kasar ta Amirka Donald Trump ya shata.

Da take magana kan wannan batu jim kadan bayan da ta fito daga zauran tattaunawar, ministar harkokin wajen kasar ta Kanada Chrystia Freeland, ta ce har yanzu ba su kai ga cimma wata matsaya ba.

Sai dai da yake magana kan wannan batu da yammacin Alhamis, Shugaban na Amirka ya ce za a cimma yarjejeniyar zuwa Jumma'a ko ma a wani lokaci, domin 'yan kasar Kanada ba su da wani zabi.