Ci-gaba da tsare Tchangari na ci wa lauyoyinsa tuwo a kwarya
May 15, 2025
A cikin wata sanarwar hadin gwiwa da lauyoyin Moussa Tchangari suka fitar ne, suka nuna damuwarsu dangane da yadda aka kwashe watanni kusan shida bayan kama dan gwagwarmayar ba tare da kotu ta kira shi domin ta saurare shi ba, ballantana a yi maganar mika shi ga hannun alkalin da zai gurfanar da shi da kuma yi masa shari'a ba. Lauyoyin suka ce wata alama ce ta kin yi wa Moussa Tchangari adalci a cikin wannan lamari. A kan haka ne suka bukaci hukumomin shari'ar da su karbe takardun karar daga hannun alkalin da ke kula da Tchangari domin mayar da su ga wani alkalin da zai iya yi masa shari'a ta adalci kuma tare da bata lokaci ba.
Karin bayani: A Nijar ana matsa kaimi domin sako fursunonin siyasa da ake tsare da su
Kaka Touda, dan fafutika kuma dangi ga Moussa Tchangari, ya nuna goyon bayansa ga yunkurin bi wa dan uwansa kadi. Su ma lauyoyin Tchangari suka ce tsare shi da ake ci gaba da yi ya saba wa doka kuma zalunci ne da keta haddin dokokin kare hakkin dan Adam na kasar Nijar da ma na kasa da kasa. Kuma Ismael Mohamed, shugaban kungiyar "Debout Niger" da ke goyon bayan mulkin sojin kasar ya ce akwai abin dubawa cikin wannan lamari, domin gudun bai wa masu adawa da mulki damar bata wa kasar suna a idon duniya.
Laifukan da ake zargin Tchangari da aikatawa
Watannin kusan shida kenan da ake tsare da Moussa Tchangari a gidan wakafi na Filingue da ke da nisan kusan kilomita 200 da birnin Yamai, a bisa zarginsa da aikata laifuka guda biyar da suka hada da cin amanar kasa da zugawa don a gudanar da ayyukan ta'addanci a kasa. To ko wani hali Moussa ke ciki a inda yake tsare? Malam Kaka Touda dan uwa ga dan gwaggwarmaya ya ba hali mai kyau ba ne.
Karin bayani: Zargin Tchangari da alaka da Boko Haram
Luyoyin dan fafutikar sun yi gargadi da kuma tuni ga alkalan kasar Nijar a game da nauyin da ya rataya a wuyansu na tafiyar da harkokin shari'a ba tare da nuna son rai ba.