Ci gaban ɓarin wuta tsaknain sojojin gwamnati da yan takife a Pakistan
October 9, 2007Kimanin dakaru 130, masu tsatsauran kishin addinin Islama, da sojoji 45 na gwamnatin Pakistna su ka rasa rayuka, a wata bata kashi da aka gwabza tsaknain ɓangarorin 2 , kusa da iyakokin Afghanistan da Pakistan.
Cemma irin wannan mummunan artabu ya wakana ranar lahadi da ta wuce, a yankin Waziristan.
A cewar kakakin gwamnatimn Pakistan, rikicin ya ɓarke bayan da wata ƙungiyar yan takife, da abkawa sojojin gwamnati, a yayin da su ke sintirin da su ka saba lokaci zuwa lokaci, domin tabbatar da tsaro.
Bayan sojojin da su ka rasa rayuka, akwai ƙarin wasu 12 da ba a gano ba har ya zuwa yanzu.
DakarunTaliban da na Alqa´ida, sun alƙawarta gama ƙarfi, domin yaƙar shugaba Pervez Masharaf da su ke ɗauka tamkar ɗan amshin shatan Amurika.
A nata gefen,ƙasar Amurika na ɗaukar yankin Waziristan, a matsayin sansanin ƙungiyoyin ta´ada, a game da haka ta ke matsa ƙaimi ga hukumomin Islamabad, su matsa lamba wajen tsarkake wannan yanki.