1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci-gaban murkushe 'yan adawa a Siriya

September 11, 2011

Ko da shi ke shugaba Bashar al-Assad na Siriya ya yi alkawarin yin sauye-sauye na siyasa, dakarunsa sun tsananta daukar matakan murkushe 'yan zanga-zangar neman sauyi

'Yan zanga-zangar neman sauyi a SiriyaHoto: AP

Dakarun tsaron Siriya sun tsananta daukar matakan murkushe masu boren kin jinin gwamnati a birnin Homs kwana daya bayan da aka rawaito shugaba Bashar al-assad yana mai daukar alkawarin gudanar da sauye sauye. Shugabannin adawar kasar sun ce an tura dakarun tsaro zuwa birnin Homs inda suka bude wutar kan mai uwa da wabi. Ba a dai samu rahoton da ke nuni da wadanda suka mutu ko kuma suka jikata ba. A ma rana Asabar 10.09.2001 akalla farar hula 24 suka rasa rayukansu a wuraren daban daban a kasar Siriya mafi yawansu a birnin Homs . 'Yan fafutukar kare hakkin bil Adama a kasar sun ce akwai kuma wasu dakarun soja da ke kai samame a lardin Idlib da ke yankin arewa maso yammacin kasar .

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Yahouza Sadissou Madobi