1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaban rikicin Irak

February 28, 2006

Tashe tashen hankulla babu ƙaƙƙabtawa, na ci gaba da hadasa asara rayuka a ƙasar Iraki.

A ranar yau talata, wasu yan ƙunar baƙin wake sun kai tagwayen hare hare a birnin Bagadaza.

Mutane kimanin 30 sun rasa rayuka, sannan da dama, sun ji mumuman raunuka.

Bugu da ƙari wani hari makamancin wannan ,ya wakana a tsakiyar kasuwar garin Karrada, wanda shima ya jawo assara rayuka 4.

Daga barkewar rikicin addinin ranar laraba da ta wuce, zuwa yanzu, mutane kussan 400 su ka rasa rayuka.

A ɓangasen siyasa kuma, wani rikici ya kunnu tsakanin Shugaban ƙasa Jallal Talabani ,da Praminista Ibrahim Jafari.

Shugaban ƙasar, ya zargi Praminista, da kai ziyara a ƙasar Turquia, ba tare da ya sanar da shi ba.

Ibrahim Aljaafari, ya tantana da takwaran sa, Tayib Erdowan, a game da tashe tashen hankulla da ke wakana a ƙasar Irak, tsakanin yan sunni day an shi`a.

Pramistan Turquia, ya gayyaci ƙasashen yanki baki ɗaya, da su bada haɗin kai, a samo ruwan kashe wannan wuta, wace idan ta ci gaba, za ta yaɗuwa a dukkan ƙasashen yankin.