Ci-gaban zanga-zanga a Masar
January 26, 2011![](https://static.dw.com/image/6418450_800.webp)
A ƙasar Masar an yi arangama tsakanin 'yan sanda da masu zanga zanga a tsakiyar Alƙahira babban birnin ƙasar da kuma birnin Suez da ke gabar tekun kasar. An shiga zanga-zangar ne a rana ta biyu duk da kuwa kamen kamen da dakarun tsaro ke yi. 'Yan sanda sama da dubu 20 ne aka tura zuwa birnin na AlƘahira . An dai haramta gudanar da duk wata zanga-zanga, kuma ƙungiyoyin adawa sun ce an toshe shafukan yanar gizo na Twitter da facebook. Jami'an tsaron ƙasar ta Masar sun ce ana tsare da 'yan zanga-zanga 500. Dubun dubatan jama'a ne dai suka shiga zanga-zangar domin yin kira ga ɗan kama karya Shugaba Hosni Mubarak da ya sauka daga karagar mulki.
Shafukan yanar gizo na ƙasar ta Masar da na sauran ƙasashen Larabawa na ba da rahotannin da ke nuni da arcewar ɗan shugaba Mubarak Gamal da iyalinsa zuwa ƙasar Birtaniya a asirce. Ministan harkokin wajen Jamus, Guido Westerwelle ya ce gwamnatin Jamus na nuna matuƙar damuwa da rikicin da ake yi a kasar ta Masar tare da yin kira ga dukkan bangarori da su kauce wa tsunduma kasar a cikin tashin hankali.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Ahmad Tijani Lawal