1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci-gaban zanga-zanga a Siriya

September 7, 2011

Faransa ta soki kasar Siriya da cin zarafin bil Adama bayan da dakarunta suka halaka mutane 12 a ci-gaban zanga-zangar nuna adawa da gwamnati

Tankar soja a birnin HomsHoto: picture alliance/dpa

A matsayin martaninta game da matakan murkushe 'yan zanga-zanga da dakarun Siriya ke dauka inda suka halaka mutane 12, tara daga cikinsu a cikin wani samame da suka kai a birnin Homs, Faransa ta soki kasar ta Siriya da cin zarafin bil Adama. A dai halin da ake ciki yanzu Siriya ta yi kira ga Shugaban kungiyar kasahen Larabawa, Nabil al Arabi da ya dakatar da ziyarar da ya yi shirin kai mata har illa ma shaallahu. Shugaba Bashar al-Assad ya nuna rashin jin dadinsa game da shirin zaman lafiya da ake sa ran al-Arabi zai gabatar yayin ziyarar tasa. A wani taro da suka gudanar a birnin Alkahira a watan Agusta ne ministocin harkokin wajen kungiyar ta kasashen larabawa suka tsai da shawarar gabatar da wannan shiri .

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Aliyu