1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cijewar tattaunawa tsakanin Isra'ila da Falasɗinawa

February 9, 2011

Rasha ta buƙaci Kwamitin Sulhu da ya kai ziyara Gabas Ta Tsakiya da zumar maido da shawarwarin zaman lafiya bisa kan turba.

Har yanzu duk ƙoƙarin sake ganawa kai tsaye ya ci-turaHoto: picture-alliance/dpa

A wani mataki dake da nufin farfaɗo da tattaunawar zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falasɗinawa da ta cije, Rasha ta buƙaci Kwamitin Sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya da ya yi tattaki zuwa Gabas Ta Tsakiya. A dangane da wannan kwan gaba kwan baya da kuma halin da ake ciki a yankin, jakadan Rasha a Majalisar Ɗinkin Duniya Vitaliy Tschurkin ya ce shigar da kwamitin sulhun cikin tattaunawar kai tsaye za ta taimaka domin cimma manufar da aka sa a gaba. Jakadan yayi tuni da cewa tun bayan shekarar 1979 Kwamitin Sulhun bai sake kai wata ziyara a Gabas Ta Tsakiya ba.

"Mun ba da wannan shawara yanzu saboda mun damu game da halin da ake ciki a Gabas Ta Tsakiya. Kamar yadda muka sani duk ƙoƙarin sake fara tattaunawa gaba da gaba tsakanin Isra'ila da Falasɗinawa ya ci-tura."

A wasu hare-haren da sojojin sama na Isra'ila suka kai a Zirin Gaza, sun jiwa mutane takwas rauni. Isra'ila ta ce harin ramuwa ne ga wasu hare-haren rokoki da aka kai kanta daga yankin Falasɗinawa. Hakazalika hare-haren sun kuma wani sansani da ake zargi Baradan ƙungiyar Al-Kuds na amfani da shi wajen horas da sojojin sa kai.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu