Cika shekara guda da kai hare haren ta´addanci a London
July 7, 2006Talla
A yau an yi tsit na tsawon mintuna biyu a duk fadin Birtaniya don tunawa da cika shekara daya da kai hare haren ranar 7 ga watan yulin shekara ta 2005 a birnin London. Hare haren wadanda wasu musulmi ´yan Birtaniya su 4 suka kai akan hanyoyin sufurin London sun yi sanadiyar mutuwar mutane 52 da kuma maharan kansu. FM Tony Blair da jami´an ´yan sanda da kuma wadanda suka tsira daga hare haren sun hallara a wasu wuraren ibada da aka tanadar na musamman don bukin na yau. FM Blair da kuma shugaban ´yan sandan birnin London Ian Blair sun yi gargadi game da kai sabbin hare hare. A ranar 7 ga watan yulin bara wasu musulmin Birtaniya su hudu suka ta da bama bamai a cikin jiragen karkashin kasa da kuma cikin wata safa a babban birnin na Birtaniya.