1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cika shekaru biyu da cafke Laurent Gbagbo

April 11, 2013

Shekaru biyu bayan cafke tsohon shugaban ƙasa Laurent Gbagbo, har yanzu muƙarrabansa na ƙulle ba tare da sun fuskanci shari'a ba.

Former Ivory Coast President Laurent Gbagbo attends a confirmation of charges hearing in his pre-trial at the International Criminal Court in The Hague February 19, 2013. Gbagbo is charged with crimes against humanity committed during the 2011 civil war sparked by his refusal to accept the election victory of rival Alassane Ouattara. REUTERS/ Michael Kooren (NETHERLANDS - Tags: POLITICS CRIME LAW)
Laurent Gbagbo a Kotun hukuntan manyan laifukan yaƙi ta ICCHoto: Reuters

A wannan alhamis tsohon shugaban ƙasar Côte d'Ivoire Laurent Gbagbo da muƙarrabansa ke cika shekaru biyu da shiga hannun hukumomi bayan da suka shafe makonni biyu a jere suna musayar wuta da dakaru a Abidjan. Wannan kamu shi ne ya kawo ƙarshen rikicin bayan zaɓen da ya ɓarke a zaɓen na watan Nuwamban shekarar 2010 inda alƙaluman da aka bayyanar a hukumance suka ce mutane dubu uku suka hallaka kana wasu ɗaruruwa kuma suka rasa matsugunnensu.

Shekaru biyu kenan da wasu jiga-jigan tsohuwar gwamnatin ke tsare a gidan kasson da ke Abidjan da ma wasu gidajen yarin da ke cikin ƙasar ba tare da sanin ranar da za'a yi masu shari'a ba. Dakarun Faransa da na Majalisar Ɗinkin Duniya ne suka taimaka wajen cafke Gbagbo da muƙarraban nasa, a yayin da magoya bayan nasa ke kulle a gidan kaso a Côte d'Ivoire, tsohon shugaban na jiran shari'a a kotun hukunta manyan laifukan yaƙi wato ICC da ke birnin Hague.

A watan Disemban shekarar 2011, magoya bayansa sun ƙauracewa zaɓen majalisar dokokin ƙasar da aka gudanar wanda ya baiwa jami'yyar shugaban kasa Alassane Outtara ta RDR gagarumin rinjaye tare da kujeru 127 a cikin 255.

Mai ɗakin Laurent Gbagbo, SimonHoto: AP

Ina aka kwana a shari'ar bayan shekaru biyu? A wani mataki ne shari'ar ke fuskantar ƙalubale Maître Jean Sesse Bougnon ɗaya daga cikin lauyoyin da ke kare su ya yi ƙarin haske:

"Wasu laifufuka aka ɗauka aka liƙawa kowa, ba tare da an basu hujjar laifin da ake zarginsu da aikatawa ba, sai yanzu ne ake neman a lalubo laifin da ake zargin da aikatawa"

Duk rahotannin ƙungiyoyin kare haƙƙin bil Adama sun nunar da cewa laifukan da kissan da aka yi ɓangarori biyun da suka kara lokacin rikicin bayan zaɓen da ya gudana a Côte d'Ivoire. Inda a wannan watan ne ma aka tono gawawwakin wasu waɗanda aka yi wa jana'izar gama gari lokacin rikicin bayan zaɓen, wannan kuma na zuwa ne a daidai lokacin da aka wallafa wani rahoton da ya zargi shugaba Alassane Ouattara da gazawa wajen hukunta magoya bayansa da ke da hannu a rikicin, hakanan ma, masu sanya ido da dama sun gaza fahimtar yadda a yau magoya bayan tsohon shugaban ne kaɗai akewa tambayoyi.

A waje guda kuma majalisar dokokin Côte d'Ivoire ta bai shugaban ƙasa Alassane Ouattara ikon yanke shawara kan abubuwan da suka shafi tattalin arziƙin ƙasar ba tare da ya tura ƙudurin doka zuwa Majalisa ba, matakin da zai bashi damar aiwatar da shirye-shiryen da zasu tayar da komaɗar tattalin arziƙin ƙasar wacce fitowa daga kusan shekaru goma na yaƙi da rikicn siyasa.

Shugaba Alassane OuattaraHoto: AP

Ɗaya daga cikin dalilan da ya sa René Légré shugaban ƙungiyar kare haƙƙin bil Adama ta Côte d'Ivoire ya ce ya buƙaci ɓangaren shari'a da ya tabbatar ta nuna adalci kan kowa da kowa ba sani ba sabo, kuma ya buƙaci a gaggauta wannan shari'a ta magoya bayan tsohon shugaba Laurent Gbagbo

"Muna fata hukumomin shari'a su gaggauta sa'an nan kuma su gudanar da aiki cikin adalci, domin a tantance wanda ke da laifi da wanda ba yi da shi. Cigaba da tsare mutane shekaru biyu ba tare da yi musu shari'a ba wannan ba adalci ba ne kuma muna ganin ya kamata a gyara"

Haka nan kuma masu sa ido da dama na ganin cewa ana tsare waɗannan mutanen ne ba tare da ƙwararan hujjoji ba ko kuma idan aka sako su a matsayi na wucin gadi za su iya su gabatar da nasu hujjojin sai dai wasu majiyoyin kuma na zargin cewa tsanar da ake wa magoya bayan Gbagbon ne ke nuna yadda abubuwa ke gudana.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba/Julien Adayé
Edita: Usman Shehu Usman