Lafiya
Cikakken bayani game da cutar mashako
July 31, 2023![](https://static.dw.com/image/42016009_800.webp)
Talla
Mutane akalla 80 ne alkaluma suka nuna cewar sun rasa ransu a dalilin wannan cuta ta diphteria a fadin Nigeria. Sai dai hukumomi na kokarin ganin sun shawo kan yaduwarta. Daruruwan mutane sun kamu da cutar mashako a fadin Nigeria, inda aka tabbatar cewa jihar Kano ce ta zama a kan gaba a cikin jihohi masu hadari a yanzu. shin mine ne cutar Mashako wato Diphtheria? Wane rukunin mutane take kamuwa da ita? Dr. Bala Gadanga na asibitin Jami'ar Usmanu Dan fodiyo da ke Sokoto ya yi karin bayani.