1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cikas a ƙoƙarin warware rikicin Sudan

September 24, 2012

Sudan da Sudan Ta Kudu na ci gaba da taƙaddama duk da kiraye-kirayen neman shawo kan rigingimun da ke tsakanin su.

Veranstaltungs-Einladung MEDIEN INTERNATIONAL: Sudan, DW Akademie und ARD-Hauptstadtstudio

Duk da barazanar da aka yi musu cewa za a kakaba musu takunkumi ƙasasshen Sudan da Sudan Ta Kudu sun kasa warware rikicin iyaka da suka yi a tsakaninsu a tattaunawar da suka yi a jiya Lahadi. Yini guda kafin cikar wa'adin da komitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya bayar shugaba Omar Hassan al-Bashir da takwaran aikinsa na Sudan Ta Kudu Salva Kiir za su gana a birnin Addiss Ababa na ƙasar Ethiopia domin samun mafita a cikin lumana. To amma sassan da abin ya shafa sun jinginar da wannan ganawar a sakamakon wasu matsalolin da har yanzu ake fuskanta, inda wasu kafafe dake da alaƙa da wakilan ƙasashen suka ce mai yiwuwa ne a cimma matsaya a wannan Litinin .

Ƙasar Sudan da Sudan Ta Kudu da ta samu yancin kanta a shekarar da ta gabata dai, a farkon watan Agusta ne suka cimma daidaito game da taƙaddamar da suke yi akan man fetur. To sai dai har yanzu da sauran lamura da basu tantance ba game da iyaka da kuma yankin Abyei mai arzikin man fetur. Duk wani aiki na sarrafa mai da kuma sayar da shi ga ƙetare daga Sudan Ta Kudu ya dogara akan cimma yarjejeniyar samun mafita daga rikicin iyaka tsakanin ɓangarorin biyu.

Mawallafiya : Halima Balaraba Abbas
Edita : Saleh Umar Saleh