1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Cikkar ƙwanaki ɗari da fara yin tawaye a Libiya

May 29, 2011

'Yan tawayen ƙasar Libioya sun jaddda aniyar su ta kawar da mulkin kanal Gaddafi

Dakarun ƙungiyar 'yan tawayen LibiyaHoto: picture alliance/dpa

Ƙungiyar Yan 'Tawaye na ƙasar Libiya da ke gudanar da bukukuwan zagayowar cikkar kwanaki ɗari da kafuwa, ta jaddada buƙatar gani kanal Muammar Gaddafi ya sauka daga mulkin ba tare da wani sharaɗi ba.ƙungiyar wacce ta ce, wannan hanya ita kadai ce za ta sake dawo da kwanciyar hankali da kuma zaman lafiya a Libiya.

Da alama ta na yin hannun ka mai sanda ne ga ƙungiyar Tarayya ƙasashen Afirka da ke kokarin shiga tsakanin a kan rikicin.An dai shirya shugaban ƙasar Afirka ta kudu zai isa a birnin Tripoli domin gabatar da shawarwarin warware ta'adamar ga kanal Gaddafi da kungiyar ta Afirka ta tsaida.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu