1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cimma yarjejeniya kan Mai a Sudan

October 17, 2012

Majalisar Sudan ta kaɗa ƙuri'ar amincewa da yarjeniya akan harkokin Mai da makwabciyarta Sudan ta kudu

(L-R) Pagan Amum, south Sudan chief negotiator, South Sudan's President Salva Kiir, former president of Nigeria Abdulsalam Abubakar, Chief African Union mediator Thabo Mbeki, former Burundi president Pierre Buyoya and President of Sudan Omar Hassan al-Bashir meet during talks in Ethiopia's capital Addis Ababa September 24, 2012. Leaders from Sudan and South Sudan will meet on Sunday for the first time in a year to try to agree on border security so that South Sudan can start exporting oil again, a lifeline for both economies. REUTERS/Tiksa Negeri (ETHIOPIA - Tags: BUSINESS COMMODITIES POLITICS)
Hoto: Reuters

Majalisar wakilai na Sudan sun amince da yarjejeniyar da aka cimma da Sudan ta kudu kan batutuwa da suka shafi tsaro akan mai. Shugabannin kasashen biyu dake makwabtaka da juna dai sun yabawa wannan mataki da majalisar ta dauka, tare da bayyana shi a matsayin matakin kawo karshen rikicin ɓangarorin biyu dayaki ci yaki cinyewa na lokaci mai tsawo. Kakakin majalisar Sudan, Ahmed Ibrahin al-Tahir ya fadawa manema labaru a Khartum cewar, kusan dukkan 'yan majalisar ne suka amince da wannan yarjejeniyar. Fiye da rabin wakilanta 350 ne suka bayyana domin kaɗa kuri'unsu, kuma biyu ne kacal suka yi adawa da shirin.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Umaru Aliyu