1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cin hanci tsakanin 'yan sanda a Najeriya

August 1, 2012

Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta bayyana cafke wasu jami'anta 17 waɗanda ta samu suna karɓar cin hanci a shingaye daban daban da aka aika su domin tabbatar da tsaro.

A picture taken on April 18, 2011 shows Nigerian police enforcing a curfew in the capital of Bauchi state, nothern Nigeria, after riots, run by muslim youth, broke out in Bauchi. Nigeria's Goodluck Jonathan has been declared winner of presidential elections in a landmark vote that exposed regional tensions and led to deadly rioting in the mainly Muslim north. Jonathan, the incumbent and first president from the southern oil-producing Niger Delta region, won 57 percent of the vote in Africa's most populous nation, easily beating his northern rival, ex-military ruler Muhammadu Buhari. AFP PHOTO / Tony KARUMBA (Photo credit should read TONY KARUMBA/AFP/Getty Images)
Hoto: Getty Images/AFP

Da ma dai mutane da dama a jihar sun daɗe suna kokawa bisa al'adar galibin jami'an tsaron waɗanda suke tilastawa masu ababan hawa biyan wani kuɗi da baya ka'ida lamarin da ake ganin shine ƙashin bayan matsalar da rundunar ke samu na gaza shawo kan matsalar tsaro da taƙi ci taƙi cinyewa a jihar.

Tun harin watan Janairun da ya gabata a jihar Kano al'amura suka ƙi daɗin azanci, inda ako yaushe al'ummar jihar ke cikin fargaba dangane ƙaruwar tashin hankula da ake fama da ita a jihar. Galibi dai mutane na danganta kasa shawo kan wannan matsala da dabi'ar wasu daga cikin jami'an tsaro, dake aikin duba ababan hawa a shingaye daban daban a jihar bisa yadda suke barin aikin nasu suna mayar da hankali wajen karɓar cin hanci daga masu ababan hawa lamarin da ya zamo wani babban gyambo da ya hana rundunar kataɓus wajen samun nasarar yaƙin da take yi domin shawo kan matsalar tsaro da ya dabaibaye jihar.

Ɗaukar matakai don zama darasi

Tuni dai rundunar ke cewar tana ɗaukar matakai wajen daƙile wannan halayya ta ɓata gari daga cikin jami'an ta waɗanda suke fakewa da guzuma suna harbin karsana wajen tilastawa mutane bayar da cin hanci babu sidi ba sadada. Harma a kwamishinan 'yan sandan jihar ta Kano Alhaji Ibrahim Idris yace sun cafke wasu jami'ai 17 na rundunar waɗanda aka kamasu suna karɓar cin hanci daga hannun alumma, harma kuma kwamishinan ya lashi takobin sanya kafar wando ɗaya dasu.

Hoto: Katrin Gänsler

Kwamishinan ya ce "bai kamata alumma su ringa kwaɗaitawa 'yan sanda romon kuɗi ba, kuma ina kira ga al'umma duk wani ɗan sanda da yayi maka barazana ko ya nemi nagoro daga hannunka to ka yi gaggawar sanar da shelkwatar 'yan sanda domin ɗaukar mataki, za mu tabbatar mun hukunta waɗannan ɓatagari 17 ta hanyar daukar matakin da ya dace domin zama darasi ga 'yan baya."

Sai dai kuma wasu na ganin cewar wannan mataki da rundunar ta dauka cigaba ne matuka amma fa dole sai an ringa bin diddigi idan kuwa bah aka ba to zai zamo tamkar an kasha maciji ba a yanke kansa ba.Abubakar muhamd janaral shine mataimakin shugaban wata kugiya ta grassroot anticorruption initiative mai yaki da cin hanci da rashawa yace matakin zai sami nasara ne idan har za a ringa bibiya.

Shi ma a nasa ɓangaren bala abdullahishugaban kungiyar kare hakkin bil Adama ta Network for Change ya ce matakin abin na'am ne amma dai ba a yabon ɗan kuturu sai an ga ya girma da yatsa.

Hoto: Katrin Gänsler

Jama'a sun daɗe suna kokawa ga halayyar 'yan sanda

Wani abu da shi ma ke ciwa al'umma tuwo a kwarya shine batun yadda wasu 'yan sandan ke fakewa da guzuma suna harbin ta yadda suke barin aikinsu na samar da tsaro da binciken makamai suna binciken takardun motoci lamarin da shima kakakin mukaddashin kakakin rundunar 'yan sandan jihar ASP Magaji Musa Majiya ya ce ba aikin da aka sasu ba kenan.

Galibi dai al'ummar jihar kano na kallon wannan batu a matsayin wani babban ci gaba sai dai kuma abin jira a gani shine ɗorewarsa da kuma tabbatar matakin ba sani ba sabo da kwamishinan ke cewa za a ɗauka a kan wanda duk aka samu da laifi.

Mawallafi: Nasir Salisu Zango
Edita: Mohammad Nasiru Awal