1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila da Falasdinu na cin zarafi

Lateefa Mustapha Ja'afar
June 20, 2023

Kwamitin Bincike na Majalisar Dinkin Duniya, ya bayyana ci gaba da matsin lamba ga kungiyoyi masu zaman kansu da masu fafutuka da kuma kafafen yada labarai a Isra'ila da yankin Falasdinu a matsayin cin zarafin dan Adam.

Kwamitin Bincike | Majalisar Dinkin Duniya | Hakkin dan Adam
Taron Kwamitin Bincike na Majalisar Dinkin Duniya a GenevaHoto: FABRICE COFFRINI/AFP/Getty Images

Wani mamba a Kwamitin Bincike na Majalisar Dinkin Duniyar Chris Sidoti ne ya bayyana hakan yayin taron shugabannin kare hakkin dan Adam a Geneva, inda ya ce sun fuskanci an fi samun cin zarafin dan Adam din daga bangaren Isra'ila. Sai dai sun kara da cewa a yankunan Falasdinawa kamar Gabar Yamma da Kogin Jordan da kuma Zirin Gaza ma, ana samun takurawa mutane ta hanyar haramta musu taruwa waje guda ko yin gangami da ma bayyana ra'ayoyinsu. Sidoti ya kara da cewa, mahukuntan Isra'ila na kara kaimi wajen dakile hakkokin dan Adam da ma takaita ayyukan kungiyoyi masu zaman kansu a kokarin da take na ci gaba da mamaye yankunan Falasdinawa.