Cin zarafin ɗan adam a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya
September 19, 2013Sakamakon na shekara da ƙungiyar da ta fitar ya nuna gazawa ta ƙasashen duniya wajen shawo kan irn rigingimu da tashe- tashen hankula da ake fama da su a duniya. Misali halin da al' umma ta samu kanta a ciki a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Ƙungiyar ta ce bayan binciken da jami'anta suka gudanar a ƙasar sun gano cewar bradan ƙungiyar 'yan tawaye na SELEKA sun kashe ɗarurruwan rayuka na jama'a waɗanda suka haɗa da mata da yara ƙanana da tsofi waɗanda ba su ɗauke da makamai.
Lamarin tashin hankali ya fi yin ƙamari a arewacin ƙasar
Tsakanin watan Maris zuwa Yuni na wannan shekara ƙungiyar ta tsofin 'yan tawye ta lalata gidaje sama da guda dubu a birnin Bangui da kuma cikin wasu sauran ƙauyuka kusan 34 da ke kusa da birin abin da ya tilastawa wasu dubban jamaar barin gidajensu domin zuwa cikin wajen gari don gujewa tsoron kai farmaki. A cikin sanarwa babban shugaban hukumar reshen Afirka Daniel Bekele ya ce abin da ya fi takaici a cikin lamarin shi ne yadda 'yan tawayen suka yi amfanin da yara ƙanƙana dom aikata mumunar ta'asar.
A cikin dai galibin yankunan da aka gudanar da wannan cin- zarafin jama'ar babu hukumomi ko gwamna ko 'yan sanda ko kotu, sai dai kawai sojojin tsohuwar ƙungiyar 'yan tawayen ke cin karansu ba babaka.Jean Marie Fardeau na ɗaya daga cikin shugabannin ƙungiyar Human Right Watch.
Ya ce: ''Gwamnatin ba ta da cikakKen ƙarfin iko, ko da tana da shi sai dai a Bangui, wannan na ɗaya daga cikin buƙatun da muka gabatarwa gwamnatin don gauggauta naɗa hukumomin mulkin farar hula domin tabbatar da tsaro da kare hakin bil adama.''
Kira ga Majalisar Ɗinkin Duniya don shawo kan lamarin
Bincike dai na jami'an ƙungiyar wanda suka yi shi a saƙuna daban-daban na ƙasar inda suka gana da tsofin firsunoni da kuma waɗanda suka sha daga hare-haren,sun shaida cewar tun cikin watan Mayu na wannan shekara bradan ƙungiyar na SELEKA sun kashe mutane aƙalla guda 40 tare da ƙone ƙauyuka 34 kana suka riƙa yin harbi a kan mai uwa da wabi a kan farar hula tare da kwasar ganima. Sai dai Jean-Marie Fardeau ya ce tsiyar abin. ba 'yan SELEKA ba kawai ke tayar da hankali hatta suma magoya baya tsohon shugaban na ƙoƙarin haddasa ruɗani da fitina.
Ya ce: ''Halin da ake cikin a a Jamuriyar ta Afrika ta Tsakiya abin na da sarƙaƙiya saboda a kwai wasu waɗanda suka yi iƙirarin kansu da sunan sojojin da ke yin biyayya ga tsohon shugaban ƙasar dake tayar da hankali a arewacin Bangui domin yin ramuwar gayya ga ta'asar da 'yan SELEKA suka aikata.''
Sanarwar ta yi kira ga kwamitin sulhu na MDD da ya gaggauta ɗaukar matakai domin tabbatar da tsaro a cikin yankunan karkara inda jama'a ke mutuwa ba dare ba rana.
Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman