1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cin zarafin al'umma da kasar Kamaru ke yi

May 23, 2013

Amnesty International ta ce gwamnatin Kamaru na gallazawa 'yan jarida da kuma masu adawa da manufofinta.

Logo Amnesty International

Kungiyar Amnesty International ta fitar da rahotonta na shekara  inda ta nunar da cewa kamaru na daga cikin kasashen Afirka da suka fi tursasa wa 'yan adawa da 'yan jarida. Hakazalika Kungiyar da ke da mazauninta a birnin London ta ce gwamnatin Paul Biya ba ta tsinana wani abin azo a gani ba wajen inganta halin tsaron daurarru da kuma yaki da cin hanci.

Amnesty International ta nunar da cewar gwamnatin Paul Biya na ci gaba da amfani da karfin ikonta wajen cin zarafin duk wadanda ke adawa da manufofin da ta sa a gaba. Har yanzu ba ta gudanar da shari'ar 'yan arewa na SCNC da ta kame tun shekaru biyar da suka gabata ba.

Hakazalika ba da gudanar da shari'ar 'yan jarida uku da kuma wani malamin jami'a daya da ta cafke ba saboda sukar lamarin gwamnati da suka yi na amfani da fannin shari'a wajen cimma burin siyasa. Yayin da a daya hannun kuma ta ke daure da Titus Edzoa da Michel Thierry Atangana da suka yi niyyar tsayawa takarar shugabancin kasa, bayan da suka gama shan daurin shekaru 15 a gidan yari.

Magoya bayan shugaban adawa Ni John Fru NdiHoto: dapd

Bugu da kari hukumomin na Yawunde sun tarwatsa gangamin da 'yan adawa suka shirya a ranar da Paul Biya ya cika shekaru 30 akan karagar mulki, da nufin yin tir da salon mulkinsa na sai Mahdi ka ture. Alhaji Husseini waziri shugaban kungiyar SSF ta kare hakkin bil adama a kamaru ya ce akwai kamshin gaskiya a rahoton na Amnesty.

Take hakkin tsirarru a Kamaru

Ita kungiyar ta Amnesty ta yi tir da barazanar kashe jami'an kungiyoyin kare hakkin bil Adama da manyan jami'an gwamnati ke yi. Kana ta ce bai dace gwamnati ta kyale jam'a suna muzgunawa wadanda ake zargi da zama 'yan luwadi da madigo ba.

Shugaba Paul BiyaHoto: Patrick Kovarik/AFP/Getty Images

Da ma kuma kotun daukaka kara ta tabbatar da hukunci shekaru biyar a gidan yari da aka yanke Jeau Claude Roger Mbede da aka samu da laifin neman na miji kamanshi. A daya hannun kuma Amnesty international ta ce manyan gidajen yarin kamaru da ke Yawunde da Douala suna neman cika su batse, ba tare da gwamnati ta dauki matakai a kai ba. Ko da shi ma Husseini Waziri na kungiyar SSf sai da ya ce wadanda suke tsare na cikin wani mummunan hali.

Game da batun cin hanci da rashawa da ke ci gaba da katutu a kamaru kuwa, Amnesty International ta ce ci gaba irin na mai hakon rijiya aka samu, domin kuwa tsohon minista daya kawai aka yanke wa hukuncin shekaru 25 na wakafi a shekarar da ta gabata, alhali gwamnati na da jerin sunayen jami'anta da suka yi kaurin suna akan wannan batu.

Mawallafi : Mouhamadou Awal Balarabe

Edita        : Saleh Umar Saleh

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani