1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cin zarafin 'yan mata ya karu a Najeriya

April 29, 2014

A sassa daban-daban na tarayyar Najeriya ana fuskantar cin zarafi da keta hakkin mata, abin da ke tada hankali matuka.

Simbabwe Protest Frauen
Hoto: picture-alliance/dpa

Rundunar da ke aikin wanzar da zaman lafiya a jihar Filato ta ce za ta dauki matakin hukunci mai tsanani kan duk wanda ta samu daga cikin jami'an ta da laifin aikata.

Rundunar ta yi wannan kashedi ne sakamakon yadda ake samun hannun wasu jami'an wanzar da zaman lafiya a jihar da aikata fyade.

Yanzu dai aikata fyade yana neman zama ruwan dare tsakanin al'ummar Najeriya. A Filato ga misali an sami rahotannin aikata fyade daban-daban har 15, a 'yan kwanakin nan, inda a kwanan baya wani dattijo mai shekaru 70, yayi wa wata yarinya mai shekaru 13 yyade a karamar hukumar Barikin Ladi, inda a bisani bincike ya nuna ya sanya wa yarinyar kwayoyin cutar Aids ko Sida. Hakazalika a karamar hukumar ta Barikin Ladi, wani jami'in da ke rundunar wanzar da zaman lafiya a jihar mai suna Damadu Bzibu, an same shi da laifin aikata fyade, inda yayi lalata da wata yarinya mai shekaru 4 da haihuwa, lamarin da ke neman zub da mutunci da kuma martabar rundunar a idon duniya, don haka nema kakakin rundunar wanzar da zaman lafiya a jihar Filato, Keftin I.K. Iweha, ya ce "duk wanda aka samu da laifin aikata fyade, to za a kore shi nan take, kana a bisani a mika shi ga 'yan sanda domin su gurfanar da shi gaban kotu."

Hukunci mai tsanani kan masu aikata laifin fyade

Hoto: picture-alliance/Ton Koene

Wannan lamari na fyade ya soma tada hankulan jama'a a jihar, don haka nema gwamnatin jihar ta hanyar ma'aikatar mata ke neman majalisar dokokin jihar wajen ganin ta kafa dokar da za ta yi hukunci mai tsanani kan masu aikata laifin fyaden. Hajiya Gambo Alhassan Zinariya, wata jami'a ce da ke fafutikar kwato wa mata 'yanci, ta yi karin bayani game da wannan lamarin tana mai cewar "wannan matsalar dai tana mai matukar tada hankula don haka muke tashi haikkan domin ganin cewar muna yaki da wannan dabi'a ta yi wa mata fyade."

Hakan nan itama Pastor Mary Shitsay, ta ce sun dukufa kan kanfe na yaki da wannan mummunar dabi'a, "muna yunkuri cikin kungiyoyi daban-daban domin janyo hankulan iyaye mata wajen kulawa da 'ya'yansu mata."

Wannan matsala dai na barazar zama ruwa dare a fadin tarayyar ta Najeriya. Masharhanta dai sun lura cewa muddin hukumomi ba su bullo da hukunci mai tsanani ba kan masu aikata fyade, nan gaba, masu aikata laifin za su karu ne fiye da misali.

Mawallafi: Abdullahi Maidawa Kurgwi
Edita: Mohammad Nasiru Awal

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani