1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cinikayyar makamai tsakanin Siriya da Rasha

July 11, 2012

Yayin da rikicin Siriya ke ci gaba da wanzuwa Rasha ta ce za ta miƙawa ƙasar na'urorin bada kariya ta sararin Samaniya.

epa03053687 A handout photo released by the official Syrian Arab News Agency (SANA) showing crew lined up aboard Russian aircraft carrier Kuznetsov in the sea port city of Tartous in Syria on 08 January 2012. A Russian flotilla has docked at the Syrian port of Tartus in a show of solidarity with the regime of President Bashar al-Assad, Syrian state media reported. The flotilla is to stay for six days at the port, according to the report. EPA/SANA
Hoto: picture-alliance/dpa

Wani jami'in babban hukumar kula da harkokin safarar makamai zuwa ƙetare a ƙasar Rasha ya sanar- a wannan Larabar cewar Rasha ta ƙudiri anniyar miƙawa ƙasar Siriya na'urorin bada kariya ta sararin samaniya , kuma ba ta da wani shirin sanya takunkumin sayan makamai ga ƙasar ta Siriya wadda take da dangantakar ƙut-da-ƙut tun zamanin tarayyar Soviet.

Kanfanonin dillancin labarai sun ruwaito Vyacheslav Dzirkaln, muƙaddashin darektan hukumar kula da harkokin dangantaka ta fuskar soji na ƙasar Rasha yana cewar za su ci gaba da mutunta ƙwangilar da suka sanyawa hannu na baiwa Siriya na'urorin bada kariya ta sararin samaniya, kuma bai ikamata wani ya tuna cewar Rasha za ta katse hulɗar cinikayyar makamai da na fasahar soji da Siriya ba.

Wannan bayanin dai yana zuwa ne kwanaki ƙalilan bayan da jami'an gwamnatin Rasha suka sanar da cewar ba za su sake ƙulla wata yarjejeniyar cinikayyar makamai tare da ƙasar ta Siriya ba.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu