Cinikin makamashin Rasha zuwa Ukraine
January 14, 2015Ministan harkokin makamashi na kasar Rasha Alexander Novak ya bayyana cewa babu wani dalili da zai sanya a samar da sauyi a sharudan samar da makamashi a kasar Ukaraine idan sharudan da ake kai yanzu suka kammala cika aikinsu a karshen watan Maris na shekarar 2015.
Maros Sefcovic kwamishinan makamashi a Kungiyar EU yayin ganawarsa da Mista Novak a birnin Moscow ya bayyana cewa kungiyar za ta ci gaba da zama mai shiga tsakani da kan tattaunawar da ake tsakanin kasar ta Rasha da Ukraine.
Sefcovic ya ce ba za a kuma samar da tangarda ba kan shirin samar da iskar gas daga Rasha zuwa kasashen Turai da kan ratsa kasar Ukraine cikin aikin dasa sabon bututu tsakanin kasashen da zai kewaye kasar ta Ukraine.
Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Mohammad Nasiru Awal