Cocin Katolika ta sami sabon Paparoma
March 13, 2013Kadinal Kadinal na Ekkilisiyar Katolika sun zabi sabon paparoma wanda zai jagoranci mabiya darikar da adadinsu ya wuce milliyan dubu guda a duk fadin duniya.
Jama'a dai sun jinjinawa manyan mallaman Cocin wadanda suka ajiye banbance-banbancensu suka zabi paparoma na 266 a zagaye na biyar, na zabe mafi sauri a tarihin Ekilisiyar.
Dubun dubatan mabiya darikar ne suka yi dandazo a dandalin St Peter lokacin da farin hayakin ya bulbulo kana kuma aka fara kada kararrawar st Peters Basillica, nan da nan kuma mabiyan suka fara kuwan "Habemus Papam!" wanda ke nufin mun sami Paparoma a harshen Romawa na daa wato Latin .
Paparoman wanda ba'a riga an bayyana sunasa ba, zai bayyana a karon farko ta tagar da ke kallon dandalin na St.Peters domin ya yi jawabi ga mabiya darikar ta sa
Mawallafiya: Pinado Abdu Waba
Edita: Yahouza Sadissou Madobi