Comey ya zargi gwamnatin Trump da bata masa suna
June 8, 2017Tsohon daraktan hukumar ta FBI Mr. James Comey dai ya bayyana gaban kwamitin bincike na majalisar dattawan Amirka ne a wannan Alhamis dangane da zargin dakatar da binciken da ake yi wa tsohon hadimin shugaba Trump, Michael Flynn. Shi dai Mr. Flynn, an zarge shi ne da tsegunta wasu muhimman bayanan sirrin Amirka ga kasar Rasha. Mr Comey dai bai yi karin haske kan ko shugaba Donald Trump ya nemi yin karan tsaye ga tafarkin shari'a ta hanyar umartarsa da ya dakatar da binciken da ake batu a kai ba.
Zaman bin bahasin kwamitin dai ka iya yin mumunar tasiri ga shugabancin shugaba Trump, yayin da kwamitocin majalisar ke ci gaba da binciken zargin yunkurin Rasha na yin kutse cikin harkokin zaben shugabancin Amirka da aka gudanar a bara; da kuma ko kwamitin yakin neman zaben Trump na da hannu cikin badakalar.