Commonweath ta bayyana sabon jagora
April 20, 2018Shugabannin kasashe 53 renon Ingila wato Commonwealth sun amince cewar Yerima Charles ya gaji Sarauniyar Ingilar wato Sarauniya Izabes a matsayin wanda zai jagoranci kungiyar nan gaba. Shugabannin sun amince da hakan ne a wani zama da suka yi wajen birnin London a wannan Juma'a, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi kungiyar da kuma makomarta na gaba. A jiya Alhamis ne dai sarauniyar ta Ingila ta ce tana son dan nata Yerima Charles ya karbi ragamar kungiyar daga hannunta.
A jawabin da ta yi a zaman na yau, Firaministar Birtaniya Theresa May, ta ce shugabannin na da batutuwa da za su yi nazarinsu da dama, dangane da makomar kungiyar ta commonwealth. Ba a dai yi karin bayani kan lokacin da Yerima Charles din zai kama ragamar wannan kungiya ba.